Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: A wata hira da aka tambaye shi ko yana da niyyar tsayawa takarar firaminista a zabe mai zuwa, cikin karfin gwiwa ya ce: "Eh, kuma na yi imanin cewa da goyon bayan jama'a, zan yi nasara". A cewar wani rahoto da gidan talabijin na Channel 11 (Kan) na Isra'ila ya fitar, Netanyahu na kokarin mayar da ranar zaben zuwa watan Yunin 2026, watanni hudu kafin wa'adin da doka ta kayyade.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo saboda ayyukan ta’addancin majalisar ministocinsa a yakin Gaza da laifukan yaki, ya bayyana matakinsa na sake tsayawa takara a zaben 'yan majalisar dokokin Isra'ila da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamban shekarar 2026.
Your Comment